Gwamnatin Zamfara ta tsige sarkin Maru


Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige sarkin Maru, mai martaba Abubakar Chika bisa samunsa da aka yi da hannu dumu-dumu wajen taimakawa yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Har ila yau gwamnatin ta kuma tsige hakimin Kanoma, Ahmad Kanoma.

Gwamnan jihar,Bello Matawalle shine ya sanar da korar ta su cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Matawalle ya ce masu rike da sarautun gargajiyar da aka tsige za su gurfana a gaban shari’a domin su fuskanci hukunci.

Ya kara da cewa abin kunya ne a ce mutanen da aka dorawa alhakin kare al’umma amma su ne za su kasance masu ruguzata.


Like it? Share with your friends!

2
54 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like