Gwamnatin Tarayya Zata Samar Da Takin Zamani Buhu Miliyan 4 Ga Manoma 


Shirin shugaban kasa na samar da takin zamani zai samar da buhu miliyan 4 na takin zamani nau’in NPK ga manoma cikin sassaukan farashi daga nan zuwa watan Disambar shekarar da muke ciki.

Mallam Garba Shehu mai taimakawa shugaban kasa kan hulda da yan jaridu,shine ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar jiya Lahadi a Abuja.

Sanarwar dake dauke da sahannun Mista Atta Esah, mataimakin daraktan yada labarai a fadar shugaban kasa  yace Shehu ya bayyana haka ne a shirin Hannu Da Yawa, na gidan Rediyon Tarayya na Kaduna.

A cewar Shehu tsammanin da ake na samar da takin zamanin a watan Disamba, kari ne kan buhu miliyan shida da aka samar tun farkon fara shirin.

” Matsalar karancin takin zamani da kuma tsadar da yake dashi na kawo illa ga bangaren aikin noma na kasarnan.matsala ce da ta shafe shekaru an kasa magance ta, amma yanzu an samu nasara tun da aka fara aiwatar da shirin samar da takin na shugaban kasa.

“Tun lokacin da aka fara shirin, buhun takin zamani nau’in NPK mai nauyin 50kg miliyan shida ne, jihohi da kuma dillalan kayan noma suka siya a duk fadin kasarnan baki daya,”yace.

Mai taimakawa shugaban kasar yakara da cewa tsakara yawan kamfanonin hada takin zamanin daga 11 da suke a yanzu zuwa 18 kafin karshen wannan shekarar, hakan kuma zai samar da aiyukan yi 50,000.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like