Gwamnatin tarayya za ta rufe filin jirgin sama na Enugu saboda dalilan tsaro


Ministan harkokin sufurin jiragen sama,Hadi Sirika ya ce za a rufe filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu saboda dalilan tsaro.

Da yake magana ranar Juma’a a Lagos a wurin taron masu ruwa da tsaki kan harkar sufurin jiragen, ministan ya lissafo kalubalen tsaron dake damun filin jirgin da suka hada da rashin kyawun titin sauka da tashin jirgi,kusancin filin da wata kasuwa da kafa hasumiyar watsa bayanai ta gidan rediyon jihar a wurin da bai dace ba.

Ya ce kalubalen na kawo barazana ga rayukan jama’a saboda haka akwai bukatar a rufe filin jirgin.

Ya roki gwamnatin jihar da ta sauya wa kasuwar matsuguni da kuma kawar hasumiyar gidan rediyon.

Ministan ya kuma sanar da mahalarta taron cewa gwamnatin ta bawa kamfanin gine-gine na Julius Berger aikin gyaran filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos kan kudi biliyan ₦14.


Like it? Share with your friends!

1
93 shares, 1 point

You may also like