Gwamnatin tarayya za ta dawo da karɓar haraji kan katin waya


Gwamnatin tarayya zata dawo da karɓar haraji kan wasu kayayyaki amfanin yau da kullum da ake yin su a kamfanunuwan cikin gida, kamar yadda majalisar ministocin ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta yamma, ECOWAS ta umarta.

A wata wasiƙa da ministar  kuɗi, Kemi Adeosun ta aikewa da shugaban ƙasa Muhammad Buhari, ta ce sabon cajin kuɗin ba zai shafi taliyar sufageti da kuma taliya mai saurin dahuwa  nau’in su taliyar  Indomie.

Adeosun tace an cire nau’in kayan abincin biyu ne saboda suna daga cikin abinci da  da dukkanin mutane kama daga mai ƙaramin ƙarfi zuwa masu wadata kan iya siya.

Kaɗan  daga cikin kayayyakin da wannan harajin zai shafa sun haɗa da katin waya, Sabulu, takarda,turare, giya,lemuka da sauransu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like