Gwamnatin tarayya za ta ƙara girmama wasu yan Najeriya a matsayin gwarzayen dimakwaradiyya


Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa za sake fitar da karin wasu sunaye da za a bawa lambar yabo kan rawar da suka taka wajen kafa mulkin dimakwaradiya.

Sakataren ya yi wannan jawabi ne lokacin da yake jawabin bude taron bada lambar yabo ga marigayi MKO Abiola, Babagana Kingibe wanda ya yi masa takarar mataimaki da kuma marigayi Gani Fawehinmi lauyan mai fafutukar kare hakkin bil’adama.

A wurin taron bada lambar yabon, shugaban kasa Muhammad Buhari ya bawa Abiola lambar yabo ta GCFR da babban dansa Kola ya karba a madadinsa.

Ganiat Fawehinmi ta karbi lambar yabo ta GCON a madadin mijinta ya yin da Ambasada Babagana Kingibe ya karbi tasa nambar yabon da kansa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like