Gwamnatin tarayya ta kara harajin kayayyaki na VAT


Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da karin harajin kayayyaki na VTA daga kaso 5 cikin 100 ya zuwa kaso 7.2.

Zainab Ahmed,ministar kudi,kasafi da tsare-tsare ita ce ta bayyana haka ga yan jaridar dake fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar zartarwa na ranar Laraba da aka yi.

Amma kuma hakan na bukatar majalisar kasa tayi gyara kan dokar VAT ta shekarar 1994.

Idan har yan majalisun tarayya suka yarda da bukatar sabon karin zai fara aiki daga shekarar 2020.

Ahmed ta ce majalisar zartarwar ta bayar da umarni gaggauta tattaunawa da jihohi, kananan hukumomi dama sauran masu ruwa da tsaki kafin sabon karin ya fara aiki a shekarar 2020 .

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like