Gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar Zamfara


Gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar Zamfara inda aka umarci yan ƙasashen waje dake wuraren hakar ma’adanai da su gaggauta barin wuraren ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma gwamnatin ta kaddamar da wani atisaye na musamman domin kawo karshen ayyukan barayi da suka addabi jihar.

Mukaddashin babban sifetan ƴansanda na kasa,Muhammad Adamu, shine ya bayyana haka bayan kammala wani taro kan sha’anin tsaro, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Adamu ya ce za a soke lasisin duk wani kamfani ko kuma wani mutum da yaki bin wannan umarni ba tare da jinkiri ba.

“Dukkanin yan kasashen waje dake wuraren hakar ma’adanai su rufe subar wurin cikin sa’o’i 48,”ya ce.

Wannan cigaban da aka samu na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da aka gudanar da wata zanga-zanga a fadar shugaban ta Aso Rock dake Abuja kan kashe-kashen dake faruwar a jihar Zamfara.


Like it? Share with your friends!

-3
85 shares, -3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like