Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Dino Melaye a Kan Wata Sabuwar Tuhuma


A ranar Larabar data gabata 5 ga watan Disamba Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bude sabuwar shari’a akan Sanata Dino Melaye a gaban babbar kotun tarayya da ke babban irnin tarayya a Maitama,Abuja, inda ake tuhumarshi da bayar da bayanan karya akan shugaban ma’aikata na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Mista Edward Onoja.

Shari’ar na tattare da tuhume-tuhume biyu akan Melaye inda ake zarginsa da ba yan sanda bayanan karya da gangan domin batawa Onoja suna cewa yana da hannu a yunkurin kashe shi (Melaye).

Yan sandan sun bayyana cewa sun gano zargin karya da Melaye ke yi yayinda suke bincike a zargin yunkurin kashe shi a garinsa na Ayetoro-Gbede da ke jihar Kogi.

Sanatan a ranar 1 ga watan Maris, 2018 ya ki amsa laifin tuhumar da ofishin atoni janar na kasar ke yi masa a ranar 31 ga watan Janairun 2018.

Sanata Melaye dai na a kotu a ranar Laraba lokacin da Onoja ya zo ya tsaya a wajen mai bayar da shaida.

Ana zargin wanda ake karar da bayar da bayanan karya a watan Afrilun 2017 a wata hirar waya da Mista Mohammed Abubakar, dan marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Aubakar Audu, tare da kudirin bata sunan Onoja.

Onoja yace da kunnensa ya saurari hirar a shafin Saharareporters, jaridar yanar gizo.Ya bayyana cewa ya kai rahoton lamarin ga yan sanda bayan ya tuntubi yan uwansa, abokai da kuma lauyoyinsa sannan suka ce ya kai kara ga hukumar yan sanda.

Onoja yace ya kai rahoton lamarin ta wani korafi da ya rubuta ga kwamishinan yan sandaa jihar Kogi.

Justice Olasunbo Goodluck a ranar Laraba ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 14 da 28 ga watan Janairu, 2019.


Like it? Share with your friends!

-1
101 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like