Gwamnatin tarayya ta gargadi ma’aikatanta kada su shiga yajin aiki


Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya,Folasade Yemi-Esan ta gargadi ma’aikatan dake aiki karkashin gwamnatin tarayya da kada su shiga cikin yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka shirya yi a fadin kasa baki daya ranar Litinin.

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da kuma sauran kungiyoyin sun yi kira ga ma’aikata da su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin har sai gwamnatin tarayya ta janye karin wutar lantarki da man fetur da ta yi.

A wata sanarwa ranar Juma’a Yemi-Esan ta ce gwamnatin tarayya na tattaunawa da kungiyoyin wajen ganin an biya bukatun ma’aikata.

Ta kara da cewa ma’aikatan baza su iya tsunduma yajin aiki ba saboda akwai umarnin kotu da ya hana su yi.

Tun bayar sanar da shirin shiga yajin aikin ne, gwamnatin tarayya ta garzaya kotun ma’aikata inda ta nemi kotun ta hana su shiga yajin aikiin.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like