Gwamnatin tarayya ta fara amfani da jirage marasa matuki a yaki da Boko Haram


Gwamnatin tarayya ta fara amfani da jiragen sama marasa matuka a kan iyakokin kasarnan yakin da take da kungiyar Boko Haram.

An bayyana hakane cikin kunshin wani rahoto da Sani Rano, jagoran tawagar wakilan Najeriya ya zuwa majalisar dokokin kungiyar ECOWAS dake Abuja.

Rano ya ce an fara amfani da jiragen ne sakamakon karin yawan hare-hare da ake samu a yan kwanakin nan a sansanin sojoji dake yankin arewa maso gabas..

Ya kara da cewa jiragen za su rika tattara bayanan sirri domin amfanin sojojin.

A ranar Alhamis ne babban hafsan sojan kasa na Najeriya,Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa a halin yanzu yan kungiyar ta Boko Haram suna amfani da kayan yaki na zamani cikin har da jiragen sama da basu da matuka da kuma sojojin haya yan kasashen waje.


Like it? Share with your friends!

-1
98 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like