Gwamnatin tarayya ta fara aikin gadar Ibbi


Injiniyoyi da kayan aiki sun fara isa garin Ibbi dake jihar Taraba gabanin fara aikin gadar Ibbi dake kan kogin Benue.

Isowar injiniyoyin da kayan aikin sun samu tarba cikin murna daga mutanen garin da suka shafe sama da shekaru 40 suna kiraye-kirayen a gina musu gadar.

Wani mazaunin garin, Alhaji Adamu Damper ya ce al’ummar garin suna cikin farin ciki matuka da isowar injiniyoyi da kayan aiki zuwa wajen da za a fara aikin.

Alhaji Adamu ya ce mutanen kudancin Taraba, Adamawa da kuma wani bangare na jihar Borno sun shafe shekaru 40 suna kiraye-kirayen yin aikin har sai yanzu da gwamnatin tarayya ta fara aikin.

Ya kara da cewa idan aka kammala gadar zata rage nisan tafiya zuwa birnin tarayya Abuja daga jihohin dake yankin na arewa maso gabas.

A shekarar da ta wuce ne gwamnatin tarayya ta bayar da aikin gadar kan kudi naira biliyan 70.


Like it? Share with your friends!

1
59 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like