Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gaggauta biyan albashin watan Faburairu


Gwamnatin tarayya ta yi umarni da a gaggauta biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya albashin watan Faburairu domin rage radadin da sauya ranar zabe ya haifar.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ya fadawa yan jaridar dake fadar shugaban kasa haka bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta.

Lai ya ce ” An fara biyan albashi tun jiya a maimakon ranar 25 ta kowace wata da aka saba domin saukaka wahalhalun da suka taso sakamakon dage zaben.”

Idan za a iya tunawa a ranar Asabar ne hukumar zabe ta kasa INEC ta dage ranar gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisun tarayya sa’o’i kaɗan kafin al’ummar Najeriya su hallara gaban akwatunan zabensu domin kada kuri’a.


Like it? Share with your friends!

-3
126 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like