Gwamnatin tarayya ta amince a gina layin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano


Gwamnatin tarayya ta amince da a kashe dala biliyan $5.3 wajen gina layin dogo daga Ibadan zuwa Kano.

Ministan harkokin sufuri,Rotimi Amaechi shine ya bayyana haka ranar Litinin a wurin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan sufurin jiragen ruwa.

Ya ce “jiya aka amince mana muka kammala layin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano da zai lakume dala biliyan 5.3.”

Mutane da dama musamman wadanda suka fito daga yankin arewacin kasarnan sunyi kira da a fara aikin daga Kano ko kuma a fara ta duka garuruwan biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like