Gwamnatin Tarayya na shirin dawo da ‘yan gudun hijira daga Nijar


Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar wa da ‘yan ƙasar ta da ke zaman gudun hijira a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar cewa ta fara shirin dawo da su gida.

Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Babagana Zullum, shi ne ya bayyana haka a lokacin da wata tawaga ta Gwamnatin Tarayya ta kai ziyarar gani da ido ga ‘yan Nijeriya da ke gudun hijira a Diffa tare da tabbatar masu da shirin da ake yi na maida su gida.

Gwamna Zullum ya samu rakiyar Kwamishinan Tarayya na Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira Da Kula Da Baƙi ta Ƙasa (NCFRMI), Sanata Basheer Garba Mohammed, da Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Kyautata Rayuwar Al’umma ta Tarayya, Hajiya Sadiya Umar Farouq, wadda Darakta mai kula da ofishin Sakataren Dindindin na ma’aikatar ta, Alhaji Ali Grema, ya wakilta.

A lokacin ziyarar, Gwamna Zullum ya faɗa wa ‘yan gudun hijirar irin hoɓɓasan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi don ganin sun dawo gida Nijeriya lafiya lau da kuma maida su cikin sauran al’umma.

‘Yan tawagar sun kuma samu tarba daga jami’an ƙasar Nijar bisa jagorancin Gwamnan yankin Diffa, Alhaji Isa Lameen.

Haka kuma sun duba aikin gina rumfunan tafi da gidan ka guda 1,000 da ƙananan gidaje 280 don ‘yan gudun hijirar a garin Damasak wanda ke kusa da kan iyakar Nijar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like