Gwamnatin Tarayya Na Shan Caccaka Kan Karin Farashin Litar Man Fetur A Nijeriya


‘Yan Nijeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu kan karin farashin litar man fetur daga naira 160 zuwa naira 171, sakamakon kwaskwarimar da hukumar kayyade frashin albrkatun man na fetur ta kasar ta yi wa farashin man daga inda ake dakonsa, inda yanzu litar ta tashi daga naira 147.87 zuwa N155.17.

Rahotanni sun ce tuni wasu gidajen saida man suka soma kara farashin litarsu zuwa naira 170.

A jiya Juma’a 13 ga watan Nuwamba ne kuma kungiyar masu sana’o’in hannu ta Najeriya ta bi sahun masu caccakar karin farashin litar man, inda ta bayyana manufofin gwamnatin kasar kan tattalin arziki da cewar suna yiwa ‘yan Najeriya illa fiye da annobar coronavirus wajen kara jefa talakawa cikin kunci.

Yayin taron manema labarai a Abuja, babban sakataren kungiyar masu sana’o’in ta Najeriya Komolafe Gbenga ya zargi gwamnati da gazawa wajen cika alkawuran gayara matatun man kasar, don kawo karshen shigo da tataccen man daga kasashen ketare, abinda ke taka rawa wajen hauhawar farashinsa babu kakkautawa.

Gwamnatin Najeriyar dai na cigaba da kare manufofinta na janye baki dayan tallafin da take baiwa fannin sassauta farashin man a watannin da suka gabata, inda tace kasuwar man ce zata rika fayyace farashin da za a rika saida litarsa a kasar. Matakin da tace ya zama dole la’akari dafaduwar farashin gangar danyen man a duniya, abinda ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Najeriyar.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like