Gwamnatin tarayya na kashe miliyan ₦3.5 wajen ciyar da Elzakzaky a kowane wata


Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ya ce gwamnatin tarayya tana kashe miliyan ₦3.5 a kowane wata wajen ciyar da Ibrahim Elzakzaky,shugaban kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya, da akafi sani da Shi’a.

Duk da belinsa da babbar kotun tarayya ta bayar, Elzakzaky ya gaza samun yanci tun lokacin da aka kama shi a shekarar 2015.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ce ke cigaba da tsare shi a ofishin ta .

Gwamnatin tarayya ta sha nanata cewa tana cigaba da tsare Elzakzaky ne domin kare lafiyarsa saboda yana fuskantar barazana.


Like it? Share with your friends!

-2
97 shares, -2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like