Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar rage farashin litar mai


Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva ya ce tattaunawa na cigaba da gudana kan duba yiyuwar rage farashin litar man fetur.

Hakan ya ce na da alaka da faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Ya zuwa ranar Juma’a da misalin karfe tara 9:00 na dare ana sayar da gangan danyen mai nau’in Brent wanda shine ma’aunin farashi mai, kan kudi dalar Amurka $34.88 kowace ganga.

Hakan ya jawo faduwar farashin man inda yake zuwa Najeriya akan kudi ₦94 a kowace lita a cewar hukumar kayyade farashin mai PPPRA.

Idan haka ne to farashin man zai kama ₦114.53 farashin kowace lita a gidajen mai.

“Wannan batu ne dake tasowa,Muna cigaba da tuntuba, muna bin sawun batun sau da kafa tabbas farashin fetur na da alaka dana danyen mai amma muna cigaba da tuntuba zamu tuntube ku ku kara hakuri,” Sylva ya fadawa yan jaridu ranar Juma’a a Abuja.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 19

Your email address will not be published.

You may also like