Gwamnatin Tarayya :Bamu da hannu a shari’ar da ake wa El-zakzaky


Gwamnatin tarayya ta ce bata da hannu a shari’ar da ake wa, Ibrahim El-zakzaky shugaban kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da akafi sani da shi’a.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a mai magana da yawun shugaban kasa mallam Garba Shehu ya ce daga yanzu ba za su zura idanu ba kan hargitsi da magoyan bayansa ke tayarwa.

Shugaban kungiyar ta shi’a na fuskantar tuhuma ne bisa zargin da ake masa na yunkurin hallaka kansa, tara mutane ba bisa da doka ba da kuma jawowa jama’a rikici da sauran tuhume-tuhume.

Tun a shekarar 2015 El-zakzaky ke tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.

Mambobin kungiyar sun bukaci a sako shi inda suke gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja da biraen wasu jihohi da a wasu lokuta ke kai wa da rangama da jami’an tsaro har ta kai ga asarar rayuka.

Shehu ya yi kira ga yan kungiyar da kada su shiga hakin sauran jama’a inda ya ce daga yanzu gwamnati baza ta kyale su dauki doka a hannunsu ba.

Ya kara da cewa magoya bayan shugaban na shi’a su jira hukuncin da kotun dake Kaduna zata yanke kan shari’ar da ake masa.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like