Gwamnatin Taraba Ta Saka Dokar Tabaci A Jalingo Kan Barkewar Sabon Rikici….


Gwamna Darius Ishaku, na jihar Taraba, ya sanar da sanya dokar tabaci a garin Jalingo, a bisa barkewar sabon rikici a wasu Anguwanni da ke Kona da ATC da ke kusa da Jalingo.
Hakan yana cikin sanarwar da babban mai taimakawa Gwamnan a kan harkokin manema labarai, Mista Bala Dan Abu ya fitar ne.

A cewar Gwamnan, dokar tabacin za ta fara aiki ne tun daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 6 na safiya a kullum har sai abin da hali ya yi.
“A bisa dalilin barkewar sabon hargitsi a wasu anguwanni na Kona da ATC da ke kusa da Jalingo, gwamnatin Jihar Taraba ta yanke shawarar kafa dokar tabaci a Jalingo da sauran dukkanin wuraren da abin ya shafa ba tare da wani bata lokaci ba.

“Dokar tabacin za ta fara aiki ne daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 6 na safiya a kullum har sai abin da hali ya yi,” in ji shi.


Like it? Share with your friends!

-1
96 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like