Gwamnatin Rivers ta biya diyar miliyan ₦20 ga iyalan jami’an tsaron da aka kashe a zanga-zangar EndSARS


Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya sanar da bayar da diyar miliyan ₦20 ga iyalan yan sanda da kuma jami’an sojojin da aka kashe a yayin rikicin zanga-zangar EndSARS da aka yi a jihar.

Ana dai zargin ƴaƴan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra da hannu a kisan jami’an tsaron a yankin Oyigbo dake Fatakwal babban birnin jihar.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin gina dukkanin ofisoshin yan sanda da aka kone a yayin zanga-zangar ta makon da ya wuce.

Wike ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga kwamshinan yan sandan jihar da kuma wasu iyalan jami’an tsaron da abin ya shafa.

Ya bayyana kisan gillar jami’an tsaron da abun da bai dace ba wanda kuma baza a lamunta ba.

Ya kuma ci alwashin fatattakar ya’yan kungiyar ta IPOB daga jihar.

Da yake nasa jawabin kwamshinar yan sandan jihar, Joseph Mukan ya ce tuni jami’an sojoji da yan sanda suka karɓe iko da wuraren yan kungiyar ta IPOB suke da karfi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 12

Your email address will not be published.

You may also like