Gwamnatin Najeriya Ta Cire Harajin VAT, Inda Abinci, Kaya, Motoci Za Su Yi Araha A Wannan Shekarar


Kudirin tattalin arziki na shekarar 2020, ya zo da sababbin manufofi da ake sa ran za su jawowa Najeriya kudin shiga tare da zabubar da tattalin kasar, kamar yadda Jaridar The Cable ta ruwaito.

Jadawalin Wasu daga cikin amfanun wannan sabuwar dokar da ake kyautata zaton talakawan kasar Nijeriya zasu sha jarmiya.
👇👇👇

1. Motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motoci 5% daga 35%.

2. Babu haraji a kan duk ma’aikatan da albashinsu bai wuce N30, 000 ba.

3. An daina cire wani kaso da sunan kudin hatimi idan aka aika kudi a banki. Wanda aka aikawa kudin da suka kai akalla N10, 000 ne zai biya N50.

4. An rage kudin harajin da ake karba a kan kananan kamfanonin da jarinsu bai kai Naira miliyan 25 ba.

5. Gwamnati za ta karbi aron kudin da aka manta da su a cikin banki kafin wanda ya mallake su ya dawo kansu.

6. Babu VAT a kan abincin dabbobi, kayan aikin gona jiragen sama na kasuwanci da sauran kayan jirgi.

Haka zalika babu VAT a kan kudin tafiya a jirgi. Gwamnati ta cire VAT a kan filaye da gidajen da aka saida.

7. Za a rika karbar haraji a ribar da aka samu daga gudumuwa ko kyauta da gwamnati ta bada.

8. An rage mafi karancin harajin da ake karba a hannun kamfanoni daga 0.5% zuwa 0.25%.

9. Kamfanonin ketare za su bukaci lambar TIN, kuma za su rika biyan haraji.

10. Za a dauke biyan haraji daga kamfanonin da ke aikin gona da noman dabbobi da kifi.

Leave your vote

Comments are closed.

1,069 Comments

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg