Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranar Talata Da Laraba A Matsayin Hutun Bikin Sallah


Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata ga watan Mayu da Laraba 5 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu domin bikin karamar sallah.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin cikin gida, Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ta sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu ta hannun Daraktan labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Ehuriyah ta kuma jadadda cewa gwamnatin tarayya na yiwa dukkanin ‘yan Najeriya fatan za su ci gaba akan koyarwar wata mai tsarki ta hanyar yin Sadaka, da nunawa juna soyayya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like