Gwamnatin Lagos ta fara rushe gine-ginen da suka nuna alamar rugujewa.


Gwamnatin jihar Lagos ta fara rushe gine-ginen da suka nuna alamar za su iya ruguzowa a yankin itafaji dake Lagos Island.

Yanzu haka jami’an gwamnati na can a layin Freeman dake yankin Ita Faji suna gudanar da aikin rusaun.

Rushe gine-ginen na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani ginin bene mai hawa uku dake layin Massey ya rufta.

Ginin da ya rufta na dauke da makarantar firamare a hawa na biyu

Mutane 12 ciki har kananan yara 9 ne suka mutu a lamarin ya yin da aka samu nasarar ceto mutane sama da 50.

Ruftawar gini abun da yake yawan faruwa a Najeriya kuma hukumomin sun gaza shawo kan faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

-1
94 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like