Gwamnatin Laberiya ta fara raba talakawan kasar da ginin kasa inda ake gina musu na siminti


Shugaban kasar Liberia,George Weah ya kaddamar da wani shirin samar da gidajen zamani ginin siminti ga mazauna ƙauyuka dake kasar.

Shugaban ya sanar da fara shirin cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shirin ya kunshi rushe gidan kasa da mutane suke ciki inda za a gina wa mutane gida na zamani.

A kashin farko na shirin an fara da garin Sasstown kafin saura garuruwan su biyo baya.

Shugaban ya ce daga rayuwar mutane daga rayuwa a gidan kasa ya zuwa na siminti zai kawo sauyi sosai ga rayuwarsu.

Sai dai wasu yan kasar sun fara sukar shirin inda suka ce ba abune mai dorewa ba. A maimakon haka sun shawarci shugaban da ya mayar da hankali wajen bunkasa fannin kiwon lafiya da kuma samar da kayan noma na zamani cikin farashi mai sauki.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like