Gwamnatin jihar Kano, tayi watsi da rahotannin dake ikirarin cewa tana duba yiyuwar bude makarantunta.

Rahoton yayi ikirarin cewa gwamnatin ta kafa kwamiti da zai duba yiyuwar bude makarantu bayan da aka rufe su lokacin da annobar cutar Coronavirus ta barke.

Amma ma’aikatar ilimi ta jihar ta bakin mai magana da yawunta, Mallam Aliyu Yusuf ya bayyana rahoton a matsayin “labaran karya.”

Ya ce gwamnatin Kano kamar sauran jihohi ta karbi wani daftari daga ma’aikatar ilimi ta tarayya kan ka’idar da ya kamata abi kafin a bude makarantu idan lokacin da ya kamata a bude yayi.

A dalilin duba daftarin ne yasa gwamnatin jihar ta kafa kwamitin wucin gadi.