Gwamnatin Jahar Kano Zata Dauki Alaramomi 60 Aiki A Sabbin Makarantun Almajirai Na Zamani Data Gina


Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya amince da daukar Alaramma sittin (60) a matsayin Malamai da zasu karantar da dalibai a sabbin makarantun Almajirai da ya gina guda 15 a cikin jihar Kano.

Gwabnan ya bayar da wannan amincewar ne biyo bayan tattaunawa da Kwamitin Gudanar da Makarantun Alqur’ani da Islamiyya na Jihar Kano ya gabatar ta hannun Kwamishinan Ilimi Mal. Muhammad Sanusi Kiru a wannan rana.

Aikin ya kara nuna kyakkyawan kokari na gwabnan Kano wajen kawar da matsalar barace-barace da kuma samar da makarantu na Allo a cikin jihar tare da samar da kayan aikin yau da kullun kamar su gidajen kwana, gidajen kwana da kuma ingantaccen tsarin karatun da zai baiwa Almajiri Yara damar haddace Alkur’ani mai girma da kuma samun ilimi na zamani a cikin kyakkyawan tsari da aminci.

Dangane da wannan ci gaba, za’a gabatar da Alaramma 60 na makarantu guda uku (3) na sabbin makarantun Almajiri da ke Bunkure, Kanwa a Madobi da Kiyawa a karamar hukumar Bagwai bandasu za’a gina a kowacce karamar hukuma


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like