Gwamnatin Borno za ta samar da Ruga a Dajin Sambisa


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da wani bangare na Dajin Sambisa domin ayi amfani da shi wajen shirin samar da wurin kiwo ga fulani makiyaya.

Zulum ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da Shehun Borno, ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a gidan gwamnati dake Maiduguri.

Gwamnan ya ce gandun dajin da aka shata domin kaddamar da shirin ya fada kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza, Chibok, Damboa da kuma Askira-Uba.

Ya kara da cewa tuni aka tattaro jami’an hukumar samar da tsaro ta Civil Defense da masu kula gandun daji da kuma mafarauta domin su bawa yankin kariya daga barazana tsaro.

Har ila yau ya ce gwamnatinsa zata sayo motocin sunturi 80 domin kare makiyaya da kuma manoma.


Like it? Share with your friends!

-2
72 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like