Gwamnatin Bauchi za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na ₦30,000


Gwamnatin jihar Bauchi ta amince a farar biyan mafi ƙarancin albashi na ₦30,000 ga ma’aikatan jihar.

Sanarwar fara biyan mafi ƙarancin albashin na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muhammad Baba ya fitar ranar Laraba.

A cewar sanarwar fara biyan mafi karancin albashin zai fara ne nan take daga 1 ga watan Janairu 2020.

Amincewa da fara biyan mafi karancin albashi ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa kan aiwatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like