Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya bayyana wa majalisar dokokin kasar cewa gwamnati ta tura jami’an tsaro 25,000 domin tabbatar da kawo karshen tashe-tashen hankula da wasoson duniyar jama’a da ake fuskanta a kasar.

Gwamnatin ta ce kimanin mutane 210 suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankulan. Wannan tashe-tashen hankula sun samo asali bisa matakin wata kotu na daure tsohon Shugaban kasar Jacob Zuma na watanni 15 saboda saba umurnin kotu, amma a yankin KwaZulu-Natal kadai inda Zuma ya fito kusan mutane 100 tashe-tashen hankulan suka halaka.

Tsohon Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu duk zarge-zarge cin hanci da yake fuskanta talakawa suna ganin sa a matsayin kwarzo mai kare musu hakki.