Gwamnati Ta Sha Alwashin Cin Gaba Da Wallafa Sunayen Barayin Gwamnati


Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya jaddada cewa babu wata barazana da za ta firgita gwamnatin tarayya kan shirinta na ci gaba da wallafa sunayen barayin gwamnati.

Ministan ya nuna cewa tun da farko, jam’iyyar PDP ce ta kalubalanci gwamnati kan ta fitar da sunayen barayin gwamnati inda ya kalubalanci duk wanda aka saka sunansu kan ya je kotu idan yana ganin an bata masa suna ne.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like