Gwamna Yari ya gana da Osinbajo


Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, ya gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Gwamnan ya isa fadar Aso Rock da misalin karfe 2:04 inda ya zarce kai tsaye ya zuwa ofishin mataimakin shugaban kasar domin fara ganawar.

Ganawar ta mutanen biyu ta gudana cikin sirri.

Gwamna Yari na daya daga cikin gwamnonin uku da basu gamsu da salon jagorancin shugaban jam’iyar APC na kasa, Adams Oshimhole kan zabukan fidda gwanin jam’iyar da aka gudanar.

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da kuma na jihar Ogun Ibikunle Amosun sune sauran gwamnonin biyu da suke da matsala da Oshimhole.


Like it? Share with your friends!

2
73 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like