Gwamnan Oyo ya kamu da Coronavirus


Gwamnan jihar Oyo,Seyi Makinde ya kamu da cutar Coronavirus kuma tuni ya killace kansa.

Makinde ya bayyana haka ne cikin wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.

Gwamnan ya ce bai nuna wasu alamomi dake nuna cewa yana dauke da ciwon ba kuma ya ce zai cigaba da killace kansa.

Gwamnan ya kuma ayyana sunan, Farfesa Temitope Alonge a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar Coronavirus a jihar.

Makinde ya zamo gwamna na uku da ya kamu da cutar Coronavirus bayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma na Bauchi, Bala Muhammad.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like