Gwamnan jihar Ondo,Rotimi Akeredolu wanda ya kamu da cutar Korona a makon da ya wuce ya sanar da warkewarsa daga cutar.

A wani taron manema labarai a Akure babban birnin jihar ranar Litinin, gwamnan ya ce likitoci sun tabbatar masa da cewa baya dauke da cutar biyo bayan gwajin da aka yi masa har sau biyu da ya nuna hakan.

Gwamnan ya ce a yau Litinin ne ya samu sakamakon gwajin da aka yi masa.

Akerodulu ya godewa Allah kan rahamar da ya yi masa da mutane yan asali da ma mazauna jihar kan kauna da suka nun masa ta hanyar yi masa addu’ar samun lafiya.