Gwamnan Niger ya warke daga cutar Korona bayan mako guda a killa ce


Gwamnan jahar Niger, Abubakar Sani Bello, ya warke daga cutar Korona mako guda bayan da ya sanar da ya kamu da cutar.

Bello ya sanar da ya kamu da cutar ne ranar 9 ga watan Nuwamba.

Amma kuma cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin gwamna ya sanar da warkewarsa zagaye cutar.

“Ina farin cikin sanar daku cewa na warke daga cutar Covid19. Na gode muku da addu’a da kuma fatan alkhairinku a tsawon wannan lokaci,” ya ce.

Gwamna Bello ya shiga cikin sahun wasu jerin gwamnonin jihohin kasarnan da suka kamu da cutar suka warke.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like