Gwamnan Kebbi ya bada umarnin biyan ma’aikatan jihar albashinsu na watan Yuni


Gwamna Atiku Bagudu,na jihar Kebbi ya bada umarnin gaggawa da abiya ma’aikatan jihar da kuma na kananan hukumomin, albashinsu na watan Yuni

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa, da sakataren yada labaran gwamnan, Abubakar Dakingari ya fitar aka kuma rabawa manema labarai a birnin Kebbi.

Sanarwar ta rawaito sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri na cewa an yi hakan ne domin ma’aikatan jihar su samu damar yin bikin sallah tare da iyalinsu cikin farin ciki da walwala.

Gwamnan ya kuma yi wa ma’aikatan fatan yin bikin lafiya.

Yin hakan ya zama koyi ga abinda gwamnatin jihar Sokoto mai makotaka da jihar ta yi.

Gwamnatin ta Sokoto ta bada umarnin biyan albashin watan Yuni ga ma’aikatan jihar kana su biya ta hanyar yanka daga albashinsu a cikin watanni uku.


Like it? Share with your friends!

-1
96 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like