Gwamnan Jihar Yobe Ya Yinl Alkawarin Zama Gwamna Na Farko Da Zai Fara Tabbatar Da Tsarin Rugar Fulani


A wata ziyara da Shugabannin Kungiyar kare hakkin makiyaya ta “Miyatti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria MCBAN” reshen jihar Yobe, ta kai a gwamna Alhaji Mai Mala Buni, a fadar shi na gidan Mulki dake babbar burnin jihar, Damaturu.

Shugabannin Kungiyar karkashin jagoranci Sakataren kasa, Baba Usman Ngelzarma da Shugaban su na jiha, Alhaji Ibrahim Nangere, sun kai masa ziyarar ne a satin daya gabata, ziyarar tasu yana da nasaba da sabuwar shirin gwamnatin tarayya na Samar da Ruga a makiyaya da manufar kawo daidaito da fahimtar juna tsakanin Manoma da makiyaya.

Gwamna Mai Mala Buni yayi maraba da ziyarar tasu, kuma yayi alwashin jihar Yobe zata zama jiha ta farko da zata tabbatar da wannan tsari na samar da Ruga a makiyaya, Gwamna Buni ya bayyana wannan matakin cewa, ba karamin cigaba zai kawo a tsakanin al’ummah, makiyaya zasu samu ingantaccen rayuwa a bangaren kiwon lafiya, ilimi da samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamnan jihar, yace yana tare da wannan tsari na shugaba Muhammadu Buhari, kuma zai bada hadin kai dari-bisa-dari wajen kallon an tabbatar da tsarin samar da ruga domin a magance matsalolin rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamna Buni yayi nuni da cewa jihar sa ba’a fama da rikicin tsakanin makiyaya da manoma, amma wannan sabuwar tsari da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo, zai taimaka wajen samar da zaman lafiya musamman ma a jihohin da suke fama da matsalar rikicin makiyaya da manoma, kuma tsarin zai taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki, da samar da rayuwa mai inganci a makiyaya.

RAHOTO
MAI MALA BUNI SOCIAL MEDIA TEAM

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like