Gwamnan jihar Benue ya sauke kusan dukkanin masu rike da mukaman siyasa dake gwamnatinsa


Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sauke kusan dukkanin masu riƙe da mukami a gwamnatinsa.

Anthony Ijohor, sakataren gwamnatin jihar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Kwamishinoni hudu tare da masu bada shawara bakwai sune kadai za su cigaba da rike mukamin su a gwamnatin.

Babu wani dalili da aka bayar na sauke wasu daga cikin masu rike da mukamin a gwamnatin da Ijohor ya ce saukewar ta fara aiki nan take.

Kwamishinonin da basu taba kasa ba sun hada da na Kuɗi, Ilimi, Kimiyya da Fasaha da kuma kwamishinan Ma’adanai.

Sanarwar ta umarci kwamishinonin da su mika ragamar aikin ma’aikatan su a hannun manyan sakatarori.

Ya yin da shugabannin hukumomin gwamnati da abin ya shafa za su mika ragamar gudanar da mulkin ga darakta mafi girman mukami dake hukumar.

Gwamnan ya yaba musu kan gudummawar da suka bayar kana ya yi musu fatan alkhairi a aiyukan da za su yi anan gaba.


Like it? Share with your friends!

-1
123 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like