Gwamnan Jihar Bauchi Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe


Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a yau Talata ya amince da nada Dakta Muhammad Sambo Alkali a matsayin shugaban hukumar kula da ciwon Sida, Tarin Fuka, Kuturta da zazzabin cizon sauro ta jihar Bauchi (BACATAMA).

Haka zalika gwamnan ya kuma nada Hajiya Rakiya Saleh a matsayin shugaban Kwalejin horar da ma’aikatan jinya da kuma Ungozoma ta jihar Bauchi.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da ta fito dauke da sa hanun sakataren gidan gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Nadada Umar. Ta kardar ta karasa da cewa, wadan da aka nada wa mukaman biyu gwamnan ya umarce su da su kama aiki nan take.

Sanarwa ya fito daga Mataimaki na musamman ga gwamnan Bauchi kan harkokin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like