Gwamnan Imo ya rabawa matasa zomaye


Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya kaddamar da shirin rabon zomaye ga matasa a matsayin hanyar dogaro da kai.

Hakan na zuwa ne kasa da wata guda bayan da mai bawa gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa ya raba jakuna ga wasu matasa domin su dogara da kai.

Shi ma wani dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Anambra ba a barshi a baya domin kuwa ya rabawa mutanen mazabarsa icen rogo a matsayin tallafin dogaro da kai.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

You may also like