
Gwamnan jihar Bauchi,Bala Muhammad ya dakatar da mai martaba sarkin Misau,Alhaji Ahmed Suleiman kan rikicin da da ya jawo mutuwar mutane tara a kauyen Malunja dake Zadawa a Misau.
Har ila yau an jikkata karin mutane 6 a rikicin.
Gwamnan ya ce sarkin da Hakimin Chiroma da Dagacin kauyen Zadawa a gundumar Harɗawa da kuma sauran masu rike da masarautun gargajiya a yankin da rikicin ya faru za su cigaba da zama a dakace har ya zuwa lokacin da za a kammala bincike musabbabin faruwar rikicin.
Ya sanar da haka ne lokacin da yake kafa kwamitin bincike mai wakilai 13 kan rikici.
A ranar Litinin da Talata ne rikici ya barke a tsakanin Fulani da Manoma a kauyen Zadawa kan wani fili da ake takaddama akai inda ake zargin wasu jami’an karamar hukuma da hada baki wajen mayar da wani filin kiwo ya zuwa gona.
Comments 0