Gwamna Tambuwal ya rusa majalisar zartarwar jihar Sokoto


Gwamnan jihar Sokoto,Aminu Waziri Tambuwal ya rushe majalisar zartarwar jihar ba tare da wani bata lokaci.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na gwamnan, Mallam Abubakar Shekara yafitar.

Gwamnan ya umarci dukkanin manyan sakatarori dake ma’aikatun da abin ya shafa da su cigaba da rike ragamar ma’aikatun har ya zuwa lokacin da za a nada sababbi.

Tambuwal ya godewa tsofaffin yan majalisar zartarwar kan gudummawar da suka bayar wajen cigaban jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like