Gwamna Obasaki ya koma jam’iyyar PDP


Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya koma jam’iyar PDP.

Sanarwar komawar gwamnan jam’iyar PDP ta fito ne cikin wani sako da jam’iyar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Jam’iyar ta ce gwamnan ya sanar da komawa cikinta ne a sakatariyar jam’iyar dake jihar.

Shi ma Obasaki ya sanar da matakinsa na komawa jam’iyar PDP cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like