GWAMNA GANDUJE YA GWANGWAJE ƳAN WASAN KANO PILLARS DA KYAUTAR KUƊI DALA DUBU DAIDAI:


Saboda hazaƙar da su ka nuna wajen ciyo kofi, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya gwangwaje ƴan wasan kwallon ƙafa na (Kano Pillars) tare da shugabanninsu da kuɗi kimanin Dala Dubu ɗaya ga kowane mutum ɗaya a matsayin kyautar sharar fage kafin azo ranar da za a shirya musu babban taro na musamman a karrama su da lambobin yabo nan da ƴan wasu kwanaki kaɗan.

Ya yin da ya ke nuna farin cikinsa kan wannan nasara, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “mun ba ku wannan dala dubu ɗaya ga kowannenku, kuma ina kyautata zaton kun kai mutum (40), wannan daya ne daga cikin irin kyaututtukan da za su zo gare ku.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yau Litinin, 5 ga watan Ogusta, 2019 a Ofishinsa ya yin da ƴan wasan su ka ziyarce shi tare da magoya bayansu domin shaida masa dawowarsu da kuma gabatar masa da kofin a hukumance.

Daga ƙarshe kuma, gwamna Ganduje ya jaddada musu ƙudirinsa na cigaba da ba da gudunmawa da tallafawa ƙungiyar wasan kwallon ƙafar da kuma bunƙasa harkokin wasanni gaba daya a Jihar Kano.

Inda ya ke cewa “Kano Pillars, ita ce kungiyar wasan kwallon ƙafa mafi girma a Nageriya. Kuma dukkan ƴan Nageriya sun fahimci hakan sun kuma san hakan sarai. Ya yin da Kano Pillars ta doke Niger Tornadoes, mu na da dukkan manyan dalilai na yin murna. Yan wasanmu masu tarbiyya ne da himma gami da kishi.

“Dan haka, gwamnatinmu za ta cigaba da ba da kykkyawar kulawa kan harkokin wasanni. Kuma mun yanke shawarar samar da sabuwar ma’aikatar kula da bunkasa harkokin wasanni da matasa. Ya kuma kara da cewa mu na alfahari da matasanmu. Mu na alfahari da ku Kano Pillars, wannan nasara na nufin akwai ƙarin nasarori a gaba”.

“Sama da shekaru 60 da su ka gabata, rabonmu da wannan kofi, amma yanzu mun yi nasara sanadiyyar wannan kungiya, mu na da dukkan dalilai da za mu yi murna tare da ku. Za mu cigaba da yin dukkan mai iyuwa domin cigaban ku”.

Da ya ke nasa jawabin, Shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Suraj Shu’aibu, ya yaba tare da godewa gwamna Ganduje kan irin rawar ganin da ya ke takawa wajen ciyar da wannan kungiya gaba.

Ya kuma yi wa gwamna alƙawarin cigaba da dabbaka tarbiyya da ladabin ƴan wasansu tsawon lokacinsa. Kamar yadda ya ce “ba shakka, ƴan wasanmu su na da tarbiyya, za kuma mu cigaba da kiyayeta da habaka ta”.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like