Gwamna Ganduje Ya Ƙarfafa Hukumar Ilmi Matakin Farko A ci gaba Da Kokarin Bada Ilimi Kyauta


A cigaba da yunƙurin da ake na tabbatar da wajabcin Ilimi da ba da shi kyauta tun daga firamare har zuwa babbar sakandire, kamar yadda ya alƙawarta, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ƙarfafa hukumar Ilimi matakin farko ta Jiha (SUBEB) ta hanyar naɗa Malam Baffa Saleh Muhammad a matsayin sabon sakataren hukumar.

Malam Baffa Saleh Muhammad, tsohon malamin makaranta ne wanda ya fara aikin koyarwa a makarantar sakandiren koyar da harkokin kasuwanci ta garin Wudil a shekarar (1985). Har ya kai matsayin Daraktan kula da makarantu a hukumar ilimi matakin farko (SUBEB). Ya kuma riƙe muƙamin shugaban hukumar na riƙon ƙwarya har zuwa lokacin da mai girma gwamna ya tabbatar da naɗin Dakta Ɗanlami Hayyo a matsayin cikakken shugaban hukumar.

Kafin nan kuma, ya taɓa riƙe mukamai daban-daban a fannin Ilimi. Ya taba zama babban malami, matemakin shugaban makarantar sakandire, shugaban makarantar sakandire har sau hudu daga (1991) zuwa (2000). Ya kuma taɓa zama sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Ajingi daga (2000) zuwa (2001). Sannan kuma ya taɓa zama jami’i mai sanya ido kan makarantun firamare na Jiha daga (2001) zuwa (2004). Da sauran muƙamai da ya taɓa riƙe a fannin Ilimi.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa zaɓo mutum tsohon hannu wanda ya taba riƙe muƙamai daban-daban a harkar Ilimi irin wannan, zai taimaka matuƙa wajen cimma muradun da aka sanya a gaba ciki kuwa har da samun nasarar zamanantar da karatun allo da kuma fara aiwatar da shirin wajiabcin Ilimi da kuma ba da shi kyauta a Jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya yi imanin ƙarfafa ma’aikatun Ilimi, shi ne ginshiƙin cimma muradun da ake da su. Shi ya sa ma ya yanke shawarar naɗa sabon sakataren wannan hukuma ta (SUBEB).

Takardar wannan naɗi ta fito ne daga hannun sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ta hannun sakataren dindindin kan harkokin nazari da bincike da harkokin siyasa (REPA). Darakta Bilkisu Shehu Maimota, ta yi cikakken bayani kan yadda gwamna Ganduje ya amince da wannan naɗi na Malam Muhammad a matsayin sakataren (SUBEB).

An karanta takardar kamar haka “a yunƙurin wannan gwamnati na bunkasa hukumomin gwamnati da ma’aikatu kan gudanar da ayyuka yadda su ka kamata da samar da cigaba mai ɗorewa zuwa gaba, mai girma zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, (OFR) ya amince da naɗinka a matsayin sabon sakataren hukumar ilimi matakin farko (SUBEB) kuma naɗin naka ya fara ran 21 ga watan Yuli, 2019.

Ta cigaɓa da ƙarin bayani cewa “an kuma zaɓo ka ne an baka wannan muƙami kan la’akari da cancantarka da sahihancin takardunka da gaskiyarka da ƙwarewa da gogewarka ta aiki da hazaƙarka da kishinka gami da juriya da jajircewarka da biyayyarka da kuma irin gudunmawar da ka bayar wajen cigaban Jiharmu abar alfaharinmu.

Wannan naɗi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamna Ganduje ya himmatu wajen tabbatar da fara aiwatar da shirin wajabcin Ilimi da kuma ba da shi kyauta tun daga firamare har zuwa babbar sakandire a Jihar Kano.


Like it? Share with your friends!

1
108 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like