Tsoson shugaban kasar Najeriya, Gudluck Jonathan ya jagoranci tawagar masu sanya idanu kan zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Tanzania.

Gudluck ya jagoranci tawagar kwararru da kungiyar Tarayyar Africa (AU) ta tura domin sanya idanu a zaben.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Jonathan ya nuna ziyarar da suka kai wata mazaba dake,Dar es Salaam babban birnin kasar.

Jonathan ya ce Tarayyar Afrika na ganin zaben na yau a matsayin wata dama ga mutanen kasar ta kara karfafa dimakwaradiya da zaman lafiya a kasar baki daya