Gobarar tankar mai: Yahaya Bello ya nemi gwamnatin tarayya ta gyara tituna mallakinta dake jihar


Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gyara titunan dake karkashin kulawarta a jihar.

Bello ya mika bukatar ne biyo bayan fashewar da wata tankar mai tayi a jihar inda ta lakume rayukan mutane da dama ciki har da kananan yara yan makaranta.

Da yake magana ranar Laraba lokacin da ya ziyarci, Babatunde Fashola ministan ayyuka da gidaje a Abuja, Bello ya ce rashin kyawun da hanyoyin gwamnatin tarayya dake jihar suke ciki ya jawo haɗarurruka da dama a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Onogu Muhammad ya rawaito gwamnan na cewa gwamnatinsa tayi rawar gani wajen aikin gyaran titunan amma aikin baya da dewa saboda yawan ababen hawar dake bi ta titunan.

Bello ya shawarci ministan da ya gaggauta gyaran titunan domin kare faruwar hatsarurrukan anan gaba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like