Gobarar tankar mai ta kone dukiya ta miliyoyin naira a Lagos


An samu asarar dukiya ta miliyoyin naira bayan da wata gobara ta tashi a gadar Kara dake kan titin Lagos zuwa Ibadan.

Gobarar ta tashi ne bayan da wata tankara mai dake makare da man fetur ta yi bindiga.

Motoci da dama abin ya rutsa da su sai dai ba a samu rahoton samun asarar rayuka ba.

Gobarar tankar mai abune da ya zama ruwan dare a birnin na Lagos dama wasu sassan Najeriya da alama dai hukumomin da abin ya shafa sun gaza shawo kan lamarin.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 10

Your email address will not be published.

You may also like