Gobara ta kone wata kasuwa


Gobara ta a kone wani sashe na kasuwar Sapele dake jihar Delta.

Gobarar ta kona kayayyaki na miliyoyin naira ya yin da manyan dakunan ajiye kaya da kantuna suma basu tsira ba daga gobarar.

Wani sheda da ya ganewa idonsa abin da yafaru ya ce gobarar ta faru ne sanadiyar wutar lantarki lokacin da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Benin ya dawo hasken wutar lantarki.

Shedar gani da idon ya cigaba da cewa ” daganan a hankali ta cigaba da bazuwa sauran shaguna kafin jami’an hukumar kashe gobara su zo.”

Daya daga cikin yan kasuwar da abin ya shafa,Fejiro Onosiagbe ta roki gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki.


Like it? Share with your friends!

-1
42 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like