Gobara ta kone wani gidan mai dake kusa da filin jirgin sama na Lagos


Wani gidan mai mallakin kamfanin mai na Forte Oil dake kusa da sashen sauka da tashin jiragen sama dake zirga-zirga a cikin gida na filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos ya kama da wuta inda ya kone kurmus.

Wata motar tanka ce ta fara kamawa da wuta a lokacin da take sauke mai kafin daga bisani ta yi bindiga hakan yasa baki dayan gidan man ya kama da wuta.

Lamarin ya jawo cinkoson ababen hawa akan titin zuwa filin jirgin saman.

Wasu da abin ya faru akan idonsu sun koka kan yadda jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Lagos suka gaza kai wa gurin da abin yafaru a akan lokaci.

Gobara irin haka a gidajen mai abune da yake yawan faruwa kuma kawo yanzu hukumomin da abin ya ya shafa sun gaza shawo kan lamarin.


Like it? Share with your friends!

-2
87 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like