Gobara ta kone shaguna a kasuwar Sabo dake Shagamu


Wata gobara da ta fara da tsakar daren ranar Talata ta kone shaguna a kasuwar Sabo dake karamar hukumar Shagamu ta jihar Ogun.

Gobarar ta kama shaguna kusan 100 inda ta lalata kayayyaki da dukiya ta miliyoyin naira.

An ce gobarar ta samo asali ne sakamakon ƙaruwar hasken wutar lantarki bayan da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Ibadan ya dawo da wuta da misalin karfe daya na dare.

Wakilik jaridar Daily Trust ya gano cewa gobarar ta fara ne daga sashen masu sayar da kayan sawa kana ta bazu zuwa sauran sassan kasuwar.

Tuni dai gwamnan jihar,Dapo Abiodun da kuma basaraken yankin suka kai ziyarar jaje ga yan kasuwar da abin ya shafa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like